IQNA

Martanin Cibiyar Darul Fatawa Ta Masar Kan Kalubalantar Kur’ani Da Faransawa 300 Suka Yi

23:38 - April 25, 2018
Lambar Labari: 3482603
Bangaren kasa da kasa, Khalid Umran babban sakataren cibiyar darul fatawa ta kasar Masar, ya bayyana kiran da wasu Faransawa 300 suka yin a a cire wasu ayoyin kur’ani da cewa aiki ne na shaidanci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Almisrawi ya habarta cewa, Khalid Umran babban sakataren cibiyar darul fatawa ta kasar Masar, a wata zantawa da tashar talabijin ta “ten” ya bayyana kiran da wasu Faransawa 300 suka yin a a cire wasu ayoyin kur’ani da cewa wannan cin zarafi ne da wuce gona da iri.

Umran ya kara da cewa, dukkanin addinai da suka zo daga sama suna yin kira ne zuwa ga kadaita Allah da kuma tsayar da adalci da yada aminci a tsakanin dukaknin talaikai, wanda kuma hakan ne shi ne aiki kur’ani mai tsarki.

A Talata da ta gabata ce dai wasu fitattun mutane a kasar Faransa su 300 da suka hada da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da kuma wasu fitattun ‘yan siyasa da marubuta, suka bukaci da a cire wasu ayoyin daga cikin kur’ani, saboda abin da suka yada tsatsauran ra’ayi da wadannan ayoyin suke yi a tsakanin musulmi.

Daga cikin ayoyin hard a wadanda suke makana a kan yaki da kuma yin kakkausar suka kan ayyukan yahudawa da nasara da kuma mulhidai.

3708963

 

 

 

 

captcha