IQNA

Saboda Aiki Da Kur'ani Ne Iran Ta Iya Tsayawa A gaban Amurka Kuma Ta Samu Ci Gaba

23:39 - April 26, 2018
Lambar Labari: 3482605
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana riko da alkur'ani mai tsarki a matsayin babban makamin rinjaye a kan makiya da kuma samun ci gaba a dukkanin bangarori na rayuwa da kuma samun yardar Allah da kuma rabauta a lahira.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran ya bayyana hakan ne yau Alhamis a lokacin da yake ganawa da mahalarta gasar kur'ani mai tsarkita duniya karo na 35 da aka gudanar a birnin Tehran, da suka hada da malamai da kuma makaranta da mahardata da suka halarci gasar daga kasashen duniya 84.

Ya ce ko shakka babu daukakar musulmi tana tare da yin riko da koyarwar alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsakaka, domin kuwa manzon Allah shi ne mai fassara kur'ani ta hanyar lafazi ko kuma kuma ta hanayar aiki.

Jagora ya kara da cewa, a duk locacin musulmi suka yi riko da koyarwar kur'ani wadda ita ce hakikanin koyarwar manzon Allah, to a lokacin za su samu daukaka da 'yancin siyasarsu da lamirinsu, a duk lokacin da suka saki koyarwar kur'ani da manzon Allah, to a kafirai da sauran makiyansu za su samu galaba a kansu kuma za su zama su ne majibinta lamarinsu.

Ya ce a halin yanzu da dama daga cikin kasashen musulmi sun zama kafurai da makiya addinin mulsunci ne majibintan lamarinsu, ta fuskar siyasa da tattalin arziki, tare da mayar da shugabannin da sarakunan kasashen musulmi bayi wadanda ba su da wata kima sai dai kawai aiwatar da abin da makiya musulunci suka umarce su, kuma abin takaici shi ne, a halin yanzu makiya muslunci suna yin amfani da kasashen musulmin da kuma dukiyar kasashen musulmi wajen rusa wasu kasashen musulmi tare da haifar musu da yake-yake.

Jagora ya ce wannan duk sakamako ne na barin tafarkin kur'ani da hakikanin koyarwar manzon Allah da musulmi suka yi, kuma hakan za a ci gaba da ganin kaskanci matukar ba a koma ga Allah ba da yin aiki da umarninsa.

Haka nan kuma ya yi ishara da harin da wata kasa mai da'awar musulunci ta kai kan muuslmi a lokacin bikin aure, inda suka ragargaza wurin, da nike mata da kananan yara da makada gawawwakinsu a cikin jinni, ya ce aiki ne na makiya suka baiwa musulmi suna aiawatarwa  akan musulmi.

Kamar yadda bayyana abin da yake faruwa a Afghanistan da Pakistan da Syria da cewa, duk shiri ne na makiya muslunci da suka baiwa wasu daga cikin kasashen musulmi suna aiwatar musu kyauta.

Daga karshe ya ce dole ne musulmi su zama ickin fadaka, su mike su hada kansu, musulmi ba shi da wani wanda ya wuce dan uwansa musulmi, koda kuwa suna sabanin fahimta  a kan wata mahanga, amma dai musulunci da ya hada su guda daya ne babu sabani a kansa, addini na Allah wanda ya aiko manzon Muhammad (SAW) da shi da kuma kur'ani mai tsarki a matsayin kalamin Allah mai shiryawa.

Ya ce idan da duk musulmi za su hadu a  kan haka, to da makiya karyar ta kare, da musulmi sun zama masu izza da buwaya, da sun zama masu 'yanci a cikin dukanin harkokinsu, da sun zama al'umma mai karfin fada a ji a duniya, maimakon zama 'yan kore da 'yan amshin shata na kasashe makiya.

3709388

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna riko
captcha