Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau 21 ga watan Agusta za a gudanar da taron adduar ranar Arafah a biranen Berlin na kasar Jamus da kuma Vienna na kasar Austria.
Taron zai samu halartar musulmi daga sassa daban-daban daga wadannan birane, inda za a fara da kimanin karfe 17 na yammacin yau a agogon wadannan kasashe.
Bayan kammala karatun aduoin na ranar Arafah kuma za a gudana da sallolin magriba da isha’I a wuraren.