Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, musulmin kasar Australia sun gudanar da zaman taron tunawa da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW).
Wannan taro dai ya gudana ne a birnin Perth na kasar ta Australia, inda za a gabatar da jawabai kan tarihin rayuwar manzon Allah (SAW) da kuma abubuwan da ya hadu da sua cikin rayuwarsa mai albarka.
A kan gudanar da taron a kowace rana ta ashirin da takwas ga watan safar, wadda ta yi daidai da ranar wafatin manozn Allah (SAW) bisa ruwayoyi mafi inganci.