IQNA

Martanin Indonesia Kan Amincewar Australia Da Quds A Matsayin Birnin Isra’ila

23:58 - December 20, 2018
Lambar Labari: 3483236
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Indonesia ta mayar wa Australia da martani kan amincewa da Quds ta yamma a matsayin fadar mulkin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya Abdulharis Almashhari shugaban kwamitin kula da harkokin siyasar wajen kasar Indonesia ya mayar wa Australia da martani mai kaushi, dangane kan amincewa da Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila, inda ya ce wannana bin Allawadai dai.

Ya ci gaba da cewa, wannan matsaya da Australia ta dauka, ta kara tabbatar da cewa manyan kasashen duniya ba a shirye suke da su taimaka wajen warware rikicin Isra’ila da Palastinawa ba, maimakon hakan ma sai kara bayyana goyon bayansu suke yi a fili ga Isra’ila, duk kuwa da irin bakin zaluncin da take a kan al’ummar Palastine.

A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Indonesia ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta gaggauta amincewa da Palastinu a matsayin kasa mai cin gishin kanta.

3773960

 

 

 

captcha