IQNA

Daesh Ta Yi Da’awar Kashe Da Jikkata Wasu Sojojin Najeriya 9

19:54 - August 02, 2019
Lambar Labari: 3483905
Kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta yi da’awar kashe da jikkata sojojin Najeriya kimanin 40a  cikin Borno a wannan mako.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin Reuters ya nakalto daga shafin A’amaq na kungiyoyin ‘yan ta’adda masu akidar takfir cewa, a cikin wannan mako sun kashe tare da jikkata sojojin Najeriya 40 a cikin Jahar Borno.

Babu wata majiya da ta tababtar da wanann rahoto, amma wasu mazauna wasu kauyuka a cikin jihar Bornon sun tababtar da cewa a ranakun Litinin da Talata sojojin Najeriya sun yi bata kashi da ‘yan ta’adda.

Baya ga haka kuma ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai wasu hare-hare a  cikin wannan mako a  kan fararen hula a jihar ta Borno, inda suka kashe mutane 65 a lokacin gudanar da wata jana’iza.

 

3831555

 

captcha