IQNA

Hargisi Na Ci Gaba Da Karuwa A Yankunan Musulmin India

23:58 - February 27, 2020
Lambar Labari: 3484567
Tehran (IQNA) A ci gaba da tashe-tashen hankula a yankunan musulmi a kasar India ya zuwa yanzu mutane hudu ne suka rasa rayukansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga birnin New Delhi fadar mulkin kasar India cewa, majiyoyin asibiti a birnin sun tabbatar da cewa akalla mutane hudu sun rasa rayukansu a yau, wasu kimanin 250 kuma sun jikkata.

Tun daga ranar Lahadin da ta gabata ce daia aka fara tashe-tashen hankula a birnin na New Delhi a lokacin ziyarar shugaban Amurka, inda a halin yanzu wasu masu tsatsauran ra’ayin kyamar musulmi suke ta kai farmakia wasu unguwanni na musulmi da ke cikin birnin, inda suke lalata kaddarorin musulmi, tare da kone shaguna.

Yanzu haka dai an kafa dokar hana zirga-zirga a cikin wasu unguwannin musulmi da ke birnin, da suka hada da Chnad Bagh, Maujpour, Ja’afar Abad.

ادامه ناآرامی‌ها در مناطق مسلمان‌نشین هند + عکس

ادامه ناآرامی‌ها در مناطق مسلمان‌نشین هند + عکس

3881861

 

 

captcha