Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Laftanar Janar Jamaluddin Umar yana halartar wani taron tattaunawar sulhu tare da ‘yan tawayen Sudan a birnin Juba na Sudan ta kudu.
Rahoton ya ce, Umar ya rasu ne sakamakon tsayawar zuciyarsa daga aiki, kuma a halin yanzu haka na birnin na Juba ana gudanar da shirye-shiryen dauko gawarsa zuwa birnin Khartum.
Jamaluddin dai ya kasance tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Sudan a lokacin mulkin Umar Hassan Albashir, amma bayan hambarar da Albashir, Abdulfattah Burhan ya sanya a matsayin daya daga cikin mammbobin majalisar mulki ta kasar, daga bisani kuma ya ba mukamin ministan tsaro na kasar ta Sudan.