Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zaman taro domin duba halin da ake ciki a kasar Afghanistan, bayan da gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-Sharq Al-Awsat cewa, jami'an kasar Saudiyya na cewa, a bisa tsarin hadin kan musulmi tana ganin ya zama wajibi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin kasashen musulmi domin tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar ta Afganistan, da kuma taimakawa kasar wajen ayyukan jin kai da ya dace.
Riyadh ta jaddada cewa, tana fatan taron da Jamhuriyar ta Pakistan za ta dauki bakuncinsa a ranar 17 ga Disamba, don taimakawa wajen samar da hanyoyin da suka dace domin taimakon al'ummar Afganistan, ya zama wata hanya ta samun sauki ga al'ummar kasar.
Za a gudanar da taron ne tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, hukumomin da abin ya shafa, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa da kasashen duniya don rage tasirin rikicin matsalolin da al'ummar Afghanistan.ke ciki.