IQNA

An Sake kai Wani Harin Ta'addanci A Masallaci Domin Haddasa Fitina Tsakanin Musulmin Afghanistan

20:09 - April 23, 2022
Lambar Labari: 3487205
Tehran (IQNA) Bayanai daga Afganistan na cewa mutane kimanin 33 ne suka rasa rayukansu kana wasu 43 suka jikkata a wani harin bam da aka kai kan wani masallacin sufaye a arewacin kasar a daidai lokacin da ake sallar Juma’a.

Harin ya faru ne a masallacin Imam Sahib dake lardin Kunduz, inda masu ibadar da dama suka rasa rayukansu ciki har da yara, kamar yadda kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Harin na jiya Juma’a na zuwa ne kwana guda bayan da kungiyar IS, ta dauki alhakin kai wasu munnannen hare hare kan wasu masallatai na ‘yan shi’a dake yankin, wandanda sukayi sanadin mutuwar mutane akalla 16 da kuma raunata wasu da dama a birnin Mazar-i-Sharif dake arewacin kasar.

A watannin baya bayan nan, kasar ta Afganistan, ta sha fuskantar jerin hare-haren ta’addanci daga kungiyar mai da’awar kafa daular musulunci ta IS, mai adawa da gwamnatin rikon kwarya ta Taliban.

Iran, dake makobtaka da kasar ta Afghanistan, ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajenta ta nuna matukar damuwarta game da yawaitar hare haren da tda danganta da na rashin imani da tausayi musamman a wannan wata na Ramadana, da al’ummar musulmi ke taruwa a masallatai domin neman rahamar ubangiji.

 

4051684

 

 

 

 

captcha