Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sedi al-Balad cewa, kyakkyawar karatun wani nakasassu dan kasar Masar a wani rami da ke cikin kasuwar Khan Al-Khalil ya dauki hankula tare da jinjina wa dubban masu amfani da shafukan sada zumunta.
Shi dai wannan nakasasshe mai shekaru 50 da haifuwa, yana karatun kur’ani mai tsarki da murya mai dadi, ya karanta aya ta 21 zuwa 24 a cikin suratu Mubaraka Al-Hashr a irin salon Sheikh Tablawi, fitaccen makarancin kasar Masar.
Wannan dan kasar Masar mai shekaru 50 a duniya, da muryarsa mai dadi, ya samu yabo sosai daga wajen manyan malamai da masu karatu na kasar Masar saboda kamanceceniyar muryarsa da Sheikh Muhammad Tablawi. Dubban masu amfani da shafukan sada zumunta sun yaba da karatun nasa, muryar wannan nakasassu dan kasar Masar.