IQNA

Mutumin Da Ake Tuhuma Da Hannu A Harin Masallacin Imam Sadiq (AS) Dan Daesh Ne

23:47 - August 05, 2015
Lambar Labari: 3339492
Bangaren kasa da kasa, mutumin da ake zargin cewa shi ne ya shirya harin masallacin Imam Sadiq q (AS) a kasar Kuwait ya amsa cewa shi dan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ne.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, Abdulrahman Sabah Idan Saud wanda ake zargin cewa shi ne babban wanda ya shirya harin masallacin Imam Sadiq (AS) ranar 26 ga watan Yuni ya amsa cewa shi.

A harin mutane 27 ne suka yi shhada, yayin da wasu kimanin 227 suka samu raunuka.

Saud shi ne ya kai Sulaiman Abdulmuhsin Alquba zuwa masallacin Imam Sadiq a lokacin kai harin, kuma an kame kwanaki biyu rak bayan kai harin.

A jiya ne dai aka fara gudanar da wannan shari’a ta mutane maza 22 da kuma mata 7 wadanda ake zargin cewa suna da hannu kai tsaye a cikin wannan hari na ta’addanci.

A cikin watan Ynin da ya gabata ne babbar kotun koli ta kasar Kuwait ta sanar da cewa za ta yanke huknci kan mutane 11 daga cikin mutane da ake tuhma, yayin da sauran kuma har yanzu bas u amsa laifinsu ba.

Wannan hari dais hi ne irinsa na farko da aka kai a kasar ta Kuwait, kuma wanda ya jagoranci harin dan kasar saudiyya inda ya kashe mutane kuma ya jikkata wasu.

Mahkunta  akasar Kuwait dai sun sha alwashin bin kadun lamari domin hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan aiki na ta’addanci.

3339255

Abubuwan Da Ya Shafa: kuwait
captcha