Auguns Bashir daya ne daga cikin shugabannin kungiyar ya bayyana cewa, babbar manufarsu ita ce yada sulhu da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin dukkanin al’ummar Najeriya baki daya, wadda ta hada mabiya addinai daban-daban musamman ma dai musulunci da kiristanci.
A halin azu dai jahar Borno ita ce jaha ta farko da kungiyar ta fara aiwatar da shirinta, kuma zai ci gaba da gudana zuwa sauran jahohi a lokuta masu zuwa.
Tun a cikin shekara ta 2002 ne dai Muhammad Yusuf ya kafa kungiya wadda ke dauke da akidar wahabiyanci wadda ta rikide ta koma Boko Haram daga bisani, wadda ke kaddamar da hare-haren ta’addanci tare da kashe fararen hula da jami’an tsaro.