IQNA

An Bude Wata Cibiyar Bincike Ta Mata Kan Musulunci A Nabraska

23:24 - February 25, 2018
Lambar Labari: 3482428
Bangaren kasa da kasa, an bude wata cibiyar bincike ta mata kan msulunci a birnin Nabraska na jahar Omaha da ke kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin iric.org cewa, an bude wata cibiyar bincike ta mata kan musulunci a birnin Nabraska na jahar Omaha da ke kasar Amurka domin sanin muslunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa, babbar manufar bude cibiyar dai ita ce, bayar da dama ga mata masu son sanin addinin muslunci domin su yi bincike da kansu.

Yanzu haka dai wannan cibiya tana gudanar da ayyuaknta ba tare da wata matsala ba, kuma tana samar da dukkanin kayan bincike da ake bukata a wurin.

3694318

 

 

captcha