IQNA

Tsarin Koyar Da Kananan Yara Kur'ani A Cikin Hutun Bazara A Kuwait

23:51 - June 29, 2018
Lambar Labari: 3482796
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kur'ani ta kasar Kuwait Almanabir ta fitar da wani sabon tsari na koyar da kananan yara karatun kur'ani a lokacin hutun bazara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar kur'ani ta kasar Kuwait Almanabir ta fitar da wani sabon tsari na koyar da kananan yara karatun kur'ani a lokacin hutun bazara wanda zai fara daga wannan shekara.

Bayanin ay ci gaba da cewa tuni an riga an kammala dukkanin shirye-shirye domin fara aiki da wannan shiri, kuma shirin zai kebanci kananan yara ne 'yan shekaru 4 zuwa 9 da haihuwa.

Babbar manufar shirin dai ita ce samar da yanayi da zai taimaka wa kanan yara wajen koyon karatun kur'ani mai tsarki, da hakan ya hada har da koyar da su hardar kur'ani mai tsarki.

3726195

 

captcha