IQNA

An Gano Wani Tsohon Masallaci A Cikin Saharar Kuwait

23:53 - April 05, 2019
Lambar Labari: 3483521
Bangaren kasa da kasa, wasu masu gudanar da bincike sun gano wani tsohon masallaci a cikin saharar kasar Kuwait.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Alkhalij ya bayar da rahoton cewa, wata tawagar masu gudanar da bincike daga kasa Holland sun gano wani tsohon masallaci a cikin saharar kasar Kuwait a karkashin tarin yashi.

Tsawon bangayen masallacin ya kai mita 20 daga kowane bangare, kamar yadda kuma fadin harabarsa ta kai mita 200.

Bayanin ya ce akwai sauran ginshikan masallacin guda hudu, wadanda tsawon owanne zai kai mita daya da rabi, kamar yadda kuma aka samu mihrabin guda biyu da aka gina su a cikin masallacin.

A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje domingano shekarun ginin wannan masallaci, wanda ake ganin gininsa zai iya haura shekaru dubu daya da suka gabata.

3800942

 

 

 

 

 

captcha