Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait ta sanar ad rufe dukkanin makarantun kur'ani da cibiyoyin bincike na addini na addini a fadin kasar, domin kaucewa kamuwa da cutar corona.
Wannan mataki ya zo bayan tattaunawar da ta gudana tsakanin ma'aikatun kula da harkokin addini da kuma ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar.
Tun bayan bayyanar cutar corona a kasar, Kuwait ta bayar da hotu a dukkanin makarantun boko da suka hada da firamare da sakandare da kuma jami'oin kasar.
Wadanda kuma ake zargin cewa suna dauke da cutar an killace ana kula da sua wasu asibitoci na musamman.