IQNA

Ana Yi Wa Musulmin Da Corona Ta Kashe A Burtaniya Kabarin Bai Daya

23:57 - April 14, 2020
Lambar Labari: 3484712
Tehran (IQNA) ana hada gawawwakin musulmi da corona ta kashe domin yi musu kabarin bai daya a kudu maso gabashin birnin Landan.

Jaridar Sun ta bayar da rahoton cewa, ganin cewa adadin musulmin da suke rasa rayukansu sakamakon kamuwa da corona yana karuwa, wannan yasa cibiyoyin musulmi suna sanya ido kan yi wa musulmi kabari na bai daya.

Bayanin ya ce yanzu haka akwai musulmi kimanin 50 da ba a bizne gawawwakinsu ba, kasantuwar akwai tsare-tsare da ake bi kafin bizne mutane.

Bisa ga ka’idar musulmin Burtaniya akan rufe gawar muuslmi ne a  cikin sa’oi 24 da mutuwarsa, amma saboda tsare-satren da ake bi kafin rufe gawawwakin wadanda corona ta kashe, akwai wasu da sun kai makonni biyu ba a bizne su ba.

Richard Gomersall mai kula da makbartar ya bayyana cewa, ana rufe gawawwakin muuslmi ne bisa gat sari irin na addinin muslunci.

 

3891694

 

captcha