Shafin yanar gizo na Shafiq News ya nakalto Ali Al-Jaburi kwamandan bataliya na 42 na dakarun Hashdushabi yana bada sanarwan hakan a safiyar yau Jumma’a.
Al-Jaburi ya kara da cewa a jiya Alhamis ne dakarunsa tare da taimakon sauran jami’an tsaron kasar ta Iraqi na sama dana kasa suka fara wani shiri na tsarkake arewacin lardin Bagdaza daga mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh.
Har’ila yau Al-Jaburi ya kara da cewa mayakan na Daesh suna amfani da sansanin na karkashin kasa da ke garin Attarimiyya daga arewacin larandan Bagadaza ne don horar da mayakansu.
Banda haka ya ce dakarun da yake shugabanta sun kama mayakan na Daesh guda biyu, wadanda dama ana nemansu. Sannan an gano makamai da kuma wasu kayakin yaki a hannunsu.