IQNA

Wani Dan Majalisa A Burtaniya Ya Soki Faransa Kan Cin Zarafin Manzo (SAW)

23:37 - October 28, 2020
Lambar Labari: 3485314
Tehran (IQNA) dan majalisar Burtaniya Nazir Ahmed ya yi Allawadai da cin zarafin manzon Allah (SAW) da ake yi a kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, dan majalisar Burtaniya musulmi Nazir Ahmed ya yi Allawadai da cin zarafin manzon Allah (SAW) tare da yin kira ga masu yin hakan da su daina domin girmama musulmi kusan biliyan biyu da suke rayuwa a duniya.

Ya ce dukkanin musulmi na duniya suna daukar matsayin annabi Muhammadu fiye da matsayin iyayensu maza da mata, fiye da kowane mahaluki a duniya, a kan haka tozarta matsayinsa yana a matsayin tozarta dukkanin musulmi ne.

Ya kara da cewa, mu musulmi muna girmama dukkanin annabawan Allah, da hakan ya hada da annabi Isa (AS) da kiristoci suke girmamawa, gami da annabi Musa (AS) da yahudawa suke girmamawa, domin shi ne abin da addinin muslunci ya koyar.

Daga karshe ya kirayi mahukunta a dukkanin kasashe da su banbance tsakanin abin da ake kira ‘yancin fadar albarkacin baki da kuma cin zarafi da tozarci, musamman idan ya shafi addini ko akida, wanda rashin yin hakan zai iya haifar da rashin fahimtar juna da ma rashin zaman lafiya a tsakanin al’ummomi.

3931616

 

captcha