IQNA

Amurka Ta Kakaba Wa Wasu Daga Cikin Jagororin Ansarullah Ta Yeman Takunkumi

22:07 - February 03, 2022
Lambar Labari: 3486900
Tehran (IQNA) Amurka ta kakaba wasu daga cikin jagororin kungiyar Ansarullah da aka fi sani Alhuthi ta kunkumi.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Amurka ta kakaba wasu daga cikin jagororin kungiyar Ansarullah da aka fi sani Alhuthi ta kunkumi.

Amurka ta dauki wannan matakin da suann cewa tana bayar da kariya ga Hadaddiyar daular larabawa wadda ta fuskanci hare-haren ramuwar gayya daga dakarun kungiyar ta Ansarullah, sakamakon yadda hadadadiyar daular larabawa ta biye wa Saudiyya wajen shiga cikin yakin da Saudiyya take kaddamawra kan al'ummar kasar Yemen.

Bayan daukar matakin da Amurka ta yi na saka wasu jagororin kungiyar cikin jerin takunkuminta, ta kuma samu damar yin cinikin makamai daga hadaddiyar daular larabawa na biliyoyin dalolin da sunan tabbatar wa kasar da tsaro.

Ita ma a nata bangaren Isra'ila ta shiga wadanda suke kwadayin samun wani abu daga hadaddiyar daular larabawa, inda ita ma ta ce zata taimaka mata wajen yakin da take yia  Yemen domin a murkushe Ansarullah.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4033447

 

captcha