IQNA

Malamai Daga Najeriya sun je Nijar Domin samar da hanyoyin Sasantawa kan rikicin kasar

20:15 - August 13, 2023
Lambar Labari: 3489636
Niamey (IQNA) Tawagar malaman musulman Najeriya da za su taimaka wajen magance rikicin Nijar sun yi tattaki zuwa wannan kasa domin ganawa da shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki a kasar domin hana daukar matakin soji a kasar.

Tashar Aljazeera ta bada rahoton cewa, tawagar malamai da shugabannin cibiyoyin addinin musulunci a Najeriya sun yi tattaki zuwa kasar Nijar domin shiga tsakani domin sasanta rikicin kasar ta Nijar tare da ganawa da shugaban majalisar mulkin sojan Nijar Abdelrahman Tichiani a birnin Yamai.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce a shirye suke su tattauna da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Sabon Firaiministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ne ya bayyana ga manema labarai haka bayan tawagar Malaman Nijeriya ta ziyarci jagoran masu juyin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani ranar Asabar a Yamai.

Wannan ne karon farko da sojojin suka nuna alamar yin sulhu tun bayan da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Shugaban tawagar Malaman da suka je Yamai, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa manema labarai cewa sun je Nijar ne "domin yin sulhu"..

Sheikh Bala Lau ya ce kafin su tafi Nijar sun je wurin shugaban Nijeriya wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS Bola Tinubu inda suka gaya masa cewa bai dace a yi amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ba.

 

 

4162090

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sasantawa rikici nijar najeriya tawaga
captcha