IQNA

'Yan sanda sun kai hari kan masu tattakin Arbaeen a Najeriya

15:35 - September 05, 2023
Lambar Labari: 3489762
Abuja (IQNA) A harin da 'yan sandan Najeriya suka kai kan mahalarta muzaharar Arbaeen a birnin Zariya, an jikkata da dama daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Sahara Reporters cewa, an gudanar da muzaharar ta Arbaeen Hussaini a titunan garin Kaduna Najeriya, tare da halartar daruruwan masoya Imam Hussaini (AS) da dimbin mabiya addinin musulunci da (IMN) ta shirya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Litinin din da ta gabata a Zariya, jami’an ‘yan sanda da ga dukkan alamu sun yi wa ‘yan kungiyar IMN kwanton bauna, sun harba harsasai masu rai da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar ta Arbaeen, inda suka jikkata da dama daga cikinsu.

 Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan sanda ke kai wa ‘yan kungiyar IMN hari ba a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar,  Jami’an ‘yan sanda sun yi ta harbe-harbe da su a ‘yan watannin nan.

Ko a lokacin gudanar da wani jerin gwano a lokacin Ashura an samu irin wannan, inda jami’an tsaro suka auka wa masu jerin gwanon, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da kuma jikkatar mutane.

 

4167094

 

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya jerin gwano kaduna abuja ashura arbaeen
captcha