IQNA

Harin Isra’ila a kan Jami'ar Al-Azhar da ke Gaza

16:38 - October 12, 2023
Lambar Labari: 3489964
Gaza (IQNA) A ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kuma kai hari kan jami'ar Azhar da ke birnin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Wafa na kasar Falasdinu ya habarta cewa, a jiya Laraba jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan sun yi ruwan bama-bamai a jami'ar Azhar da kuma jami'ar Musulunci ta birnin Gaza.

Majiyoyin labarai sun ce, a wadannan munanan hare-haren, ‘yan mamaya sun lalata ginin jami’ar Musulunci gaba daya, kuma sakamakon gobara da rufe hanyar da aka yi, babu wanda ya isa ya shiga.

A daidai lokacin da jiragen saman gwamnatin sahyoniyawan su ma suka kai hari kan ginin jami'ar Al-Azhar, wanda ya yi barna mai tsanani.

A cewar majiyoyin labarai, an kuma lalata ginin cibiyar addini ta Al-Azhar.

An kara adadin shahidan Falasdinawa zuwa mutane 1100

A daidai lokacin da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da yammacin yau cewa adadin shahidai na kutsawa yankin zirin Gaza ya kai 1,100.

Har ila yau ma'aikatar ta sanar da cewa mutane dubu biyar da 339 ne suka jikkata tun farkon mamayar Gaza.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anatolia Youssef Abu al-Rish mataimakin ministan lafiya na Falasdinu a yankin zirin Gaza ya ce akasarin wadanda suka mutu da kuma jikkata mata da kananan yara ne.

Abu Al-Rish ya ce dangane da haka: Mata da kananan yara su ne kashi 60% na wadanda Isra'ila ke kaiwa hare-haren bam a zirin Gaza.

Mataimakin ministan lafiya na kasar Falasdinu ya bayyana cewa, dukkan gadajen asibitoci a Gaza sun cika kuma magunguna da na’urorin kiwon lafiya na karewa.

 

 

4174694

 

 

captcha